Dhul Hijjah 1445AH: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Kan Babbar Sallah

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da warewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishai FCT, Abuja - Majalisar olin harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta buaci alummar musulmin Najeriya da su fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah.

  • Majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya (NSCIA) ta buƙaci musulman Najeriya da su fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah
  • NSCIA ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ta buƙaci a duba jinjirin watan ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024
  • Idan aka ga watan a ranar Alhamis wacce ta yi daidai da 29 ga watan Dhul Qa'adah 1445AH, hakan na nufin ranar Juma'a za ta kasance 1 ga watan Dhul Hijjah 1445AH

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar ƙolin harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta buƙaci al’ummar musulmin Najeriya da su fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah.

NSCIA ta buƙaci a fara duba jinjirin watan na Dhul Hijjah daga ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Dhul-Qa'adah 1445AH.

Kara karanta wannan

Dhul Hijjah: Saudiyya ta fitar da sanarwa kan ranakun hawa Arfah da Babbar Sallah

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin babban sakataren NSCIA, Farfesa Salisu Shehu ya fitar a shafin yanar gizo na NSCIA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Sarkin Musulmi ya ce kan duba wata?

A cikin sanarwar NSCIA ta buƙaci al'ummar Musulmi da su fara duba jinjirin watan bayan faɗuwar rana.

A cewar NSCIA gobe Alhamis shi ne daidai da 29 ga watan Dhul-Qa'adah, 1445AH.

"Mai alfarma Sarkin Musulmi Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci al’ummar Musulmin Najeriya da su duba jinjirin watan Dhul Hijjah 1445AH bayan faɗuwar rana a ranar Alhamis 29 ga Dhul Qa’adah 1445AH (watau 6 ga watan Yunin 2024)."A kimiyance, lokacin da ake tsammanin haɗuwar watan shine ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni, 2024 da ƙarfe 1:38 na rana a agogon Najeriya." 

- Farfesa Salisu Shehu

Yaushe za a yi babbar Sallah?

Kara karanta wannan

Darajar Naira ta ragu, Dalar Amurka ta ƙara tsada a kasuwa a Najeriya

Watan Dhul-Hijjah wanda shi ne na ƙarshe a cikin watanni 12 na kalandar Musulunci, a cikinsa ne ake gudanar da Aikin Hajji.

A ranar 10 ga watan na Dhul Hijjah al'ummar Musulmi a faɗin duniya ke gudanar da Sallar layyah.

Idan aka ga watan a gobe Alhamis, hakan na nufin ranar Juma'a za ta kasance 1 ga watan Dhul Hijjah 1445AH wanda ya yi daidai da 7 ga watan Yunin 2024.

Hakan na nufin kenan za a yi Sallar Eid-el-Kabir a ranar 16 ga watan Yunin 2024.

Umarnin Sarkin Musulmi kan duba wata

A wani labarin kuma, kun ji yadda mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya umarci ɗaukacin al'ummar musulmi su fara duba jaririn watan Zhul-Qa'ada.

Sarkin musulmin ya buƙaci a fara duban jinjirin watan daga ranar Laraba, 29 ga watan Shawwal, 1445/AH wanda ya zo daidai da 8 ga watan Mayu, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboJ6f5BmnKKcXZq5brLIralmpZGeeqK4xZqpppldqK6zt8inZKato6q5rrWMsphmmqWgrqS1jJpkn5milnqlwcGaZKOhnp%2B2s7XNZq6arJGjeqW01KVkoaGan66peZBta26ZmGQ%3D

 Share!