- Fitaccen malamin addinin musulunci, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi jimamin mutuwar yayan mahaifiyarsa, Malam Abubakar Audu
- Tsohon ministan Najeriyan ya ce kawun nasa wanda aka fi sani da suna Malam Dankule ya rasu yana da shekaru 110 a duniya
- A yayin da ya ke jimamin mutuwar kawun na sa, Farfesa Isa Pantami ya yi addu'a ga iyaye da malaman da suka riga mu gidan gaskiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Tsohon ministan Najeriya kan tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya sanar da rasuwar yayan mahaifiyarsa.

Farfesa Isa Pantami wanda ya yi minista a zamanin mulkin Buhari ya ce kawun nasa, Malam Abubakar Audu ya rasu yana da shekaru masu yawa a duniya.

Kara karanta wannan
Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta
Kawun Farfesa Pantami ya rasu a Yobe
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X a yammacin yau Talata, Pantami ya ce Malam Abubakar ya rasu a garin Hausari, karamar hukumar Machina da ke jihar Yobe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar tsohon ministan:
"A yau kawun mu, yayan mahaifiyar mu, wato Malam Abubakar Audu wanda aka fi sani da suna Malam Dankule ya rasu."Allah ya dauki rayuwarsa a karamar hukumar Machina a garin Hausari da ke jihar Yobe a wurin da yake rayuwa."Farfesa Pantami ya yi wa mamacin addu'a
Sanarwar Farfesa Pantami ta ƙara da cewa Malam Dankule ya koma ga Allah ya na da sama da shekara 110 a duniya bisa kiyastawar alƙaluma.
"Allah ya sa Aljanna Firdausi ce makomarsa sa sauran iyayen mu da malaman mu da zuriyar mu."In ji Farfesa Pantami.

Kara karanta wannan
Sarautar Kano: Kungiya ta faɗi dalilin tuɓe Aminu Ado da mayar da Sanusi II da Abba ya yi
Mutane sun yi wa Pantami ta'aziyya
Ma'abota shafin X sun yi tururuwa wajen yi wa Pantami ta'aziyyar wannan rashi da ya yi.
@UmmUSerLMer:
"Allah ya gafarta mai."@AjeeyaIk:
"InnalilLahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya kai haske kabarinsa. Makocinmu ne."@jdeshikat:
"Allah ya gafarta masa. Allah ya kuma ya ba wa iyalai da abokanai hakurin rashin sa.@Madawaki_Jr:
"Allah ya gafarta ma shi ya sa ya huta da duk sauran al’umar musulmi."Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC51K2Yp51fZoJ6gZZycGajkazCr3nTrKahp55iuqq6yKyrmqZdo66rsdGisJpllpa%2Fp7HSmmSpmZ6prq61jLKYZqqRqMJw